Amurka

Clinton ta soki Trump game da Rasha

Hillary Clinton ta Democrat da Donald Trump na Republican
Hillary Clinton ta Democrat da Donald Trump na Republican REUTERS

Hillary Clinton da ke takarar shugabancin Amurka a jam’iyyar Democrat ta caccaki abokin hammayarta na Republican Donald Trump kan alakar shi Rasha. Hillary ta ce yadda Trump ke yabon shugaban Rasha barazanar tsaro ce ga Amurka.

Talla

Sai dai Trump ya ce babu wata amintaka tsakanin shi da Vladimir Putin na Rasha, kuma ba su taba zantawa ba a salula.

Amma Trump a zantawar shi da kafar NBC ya ce idan har Amurka ta tafi tare da Rasha, to mataki ne mai kyau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.