Brazil

‘Yan wasa na gujewa Wasannin Olympics saboda Zika

Sauro ke yada cutar Zika.
Sauro ke yada cutar Zika. REUTERS/Paulo Whitaker

Fargaba da ke tattare da ‘yan wasa a wasannin Olympics da za soma a Rio ita ce batun cutar zazzabin Zika inda Brazil na cikin kasashen da ke fama da matsalar a kasashen kudancin Amurka da Latin da cutar ta zama alakakai.

Talla

Sama da mutane 1,000 ke dauke da cutar Zika a Brazil.

Cizon sauro ne ke yada Cutar Zika inda ake haihuwar jaririai da karamin kai ko nakasa.

Akwai ‘yan wasa da dama da suka kauracewa zuwa wasannin a Brazil saboda tsoron cutar Zika.

Manyan zaratan ‘Yan wasa a baganren kwallon Golf da suka hada da Jason Day da Dustin Johnson da Jordan Spieth da Rory McIlroy dukkaninsun sun gujewa zuwa Brazil saboda tsoron kamuwa da Zika.

Haka ma a bangaren kwallon kwando manyan ‘yan wasan Amurka da suka hada da LeBron James da Stephen Curry da Russell Westbrook da James Harden da Chris Paul da Blake Griffin da kuma Anthony Davis sun sanar da gujewa wasannin.

‘yan wasan Tennis da dama da suka sanar da kauracewa zuwa Brazil sun hada da dan wasan Canada Milos Raonic da ‘yar wasan Romania Simona Halep Dan wasan Jamhuriyyar Czechs Tomas Berdych da kuma Karolina Pliskova.

Wasu dai kasashe sun yi wa ‘yan wasansu tanadi kafin su tafi Brazil.

Kasar Koriya ta kudu wasu tufafi na musamman ta ba ‘yan wasan da aka yi wa feshin maganin sauro domin kaucewa kamuwa da cutar Zika.

Kiyasain da aka yi maza sun fi kaucewa wasannin na Olympics a Rio sabanin Mata duk da cutar ta fi hatsari ga mata. Ana iya kamuwa da cutar ta hanyar Jima’i.

Masu shirya wasannin a Brazil sun ce baraznar Zika, ya sa mutane na kauracewa sayen tikicin shiga kallon wasannin na Olympics.

Zuwa yanzu dai babu wani rigakafin Zika, cutar da ta soma bulla a Uganda a 1947, inda a yanzu ta tsallaka zuwa kasashen kudanci da latin Amurka da kuma Caribbean.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI