Amurka

An kashe mayakan IS 45,000-Amurka

Wani Laftanar Janar a rundunar sojin Amurka Sean MacFarland ya ce rundunar hadin gwiwa da kasar Amurkan ke jagoranta ta samu nasarar kashe mayakan ISIS 45, 000 cikin shekaru biyu da suka gabata.

Sojin kasar Iraqi na samun galaba kakn IS
Sojin kasar Iraqi na samun galaba kakn IS Reuters/路透社
Talla

A cewar Laftanar Janar MacFarland ya ce cikin watanni 11 kawai rundunar hadin gwiwar kasashen ta samu nasarar kashe mayakan IS 25,000 idan kuma aka hada da 20,000 da suka kashe a baya yawansu ya kai 45,000.

Macfarland ya ce bayanan sirri da suka samu ya nuna cewa mayakan IS din da suka rage basu wuce 15,000 zuwa 30,000 bayan hasarar da yawa daga cikin manyan kwamandojinsu.

Zalika majiya daga rundunar sojin ta ce kawo yanzu mayakan na IS sun rasa kashi 50% na fadin kasar da suke iko da ita a kasar Iraqi kwatankwacin murabba’in kilomita 25,000 yayin da kuma a kasar Syria suka rasa kashi 20%.

Shekaru biyu da suka gabata ne kasar Amurka ta fara jagorantar gamayyar wasu kasashe domin murkushe mayakan na IS da suka kwace yankuna masu fadi a kasashen Syria da Iraqi.

Kawo yanzu kuma rundunar hadin gwiwar ta samu nasarar kwace garuruwan Mosul a Iraqi da Raqqa a Syria daga hannun mayakan na IS.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI