Zika

Yunkurin gano maganin cutar Zika

Cutar Zika na yaduwa ne ta hanyar cizon sauro da kuma jima'i
Cutar Zika na yaduwa ne ta hanyar cizon sauro da kuma jima'i REUTERS/Denis Balibouse

Wasu likitocin kasar Switzerland sun bukaci sauran takwarorinsu dake a sassan duniya da su tattaro bayanan Matan dake dauke da cutar Zika a wani mataki, da zai taimaka wajen binciken gano maganin cutar, dake sa haihuwar yara nakassasu.

Talla

David Baud na jami’ar Lausanne dake kasar Switzerland da kuma ke jagorantar tawagar da za su gudanar da binciken yace tattaro alkaluman mata da suka kamu da cutar Zika zai taimaka kwarai wajen gano yadda dan adam ke kamuwa da kwayar cutar da kuma yadda cutar ke yaduwa.

Mr Baud ya ce alkaluman mata masu juna biyu dake kamuwa da cutar Zika a kullum abin tayar da hankali ne inda ya shawarci likitoci da su hada kai a tattaro bayanai da soma binciken don dakile wannan cutar dake da matukar illa.

Tun bayan bullar cutar a shekarar 2015 Zika ke cigaba da bazuwa musanman a yankunan kasashen Latin Amurka da Carribean .

Binciken farko da aka gudanar bayan gano cutar Zika na nuni da cewa sauro ka dai ke iya yada cutar amman daga baya bincike ya nuna cewa zaa iya kamuwa da cutar ta hanyar Jima’I.

Cutar Zika ya fi illa ga mata masu juna biyu inda yake sa haihuwar jariri nakassasshe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.