Turkiyya

Harin bam ya hallaka mutane 30 a taron Biki

Shugaban Turkiyya Recep Tayip Erdogan
Shugaban Turkiyya Recep Tayip Erdogan REUTERS/Umit Bektas

Mutane akalla 22 suka rasa rayukan su wajen wani taron buki a kasar Turkiyya a daidai kan iyakan kasar da Syria sakamakon hari na Bam da aka kai masu. 

Talla

Harin ya jikkata mutane 94 a kauyen Gaziantep na Turkiyya dake kan iyaka da Syria.

Sanarwa daga ofishin Gwamnan yankin Ali Yerlikaya na cewa hari aka kai na Bam wajen da ake taron buki da ya janyo hasarar rayukan jama’a.

Gwamnan ya danganta harin da ayyukan ta’addanci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.