Bakonmu a Yau

Abdu Dan Naito kan rashin ilmantar da yara a duniya

Sauti 02:59
Akwai kananan yara da dama da ba sa zuwa makaranta saboda dalilai da iri-iri.
Akwai kananan yara da dama da ba sa zuwa makaranta saboda dalilai da iri-iri. UN Photo/JC McIlwaine

A wani sabon rahoton da ta fitar, hukumar kula da ilimin kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF,ta ce sama da yara miliyan 18 ne suka gagara samun ilimi a duniya,  inda kashi 40 na alkalluman suka fito daga yankunan Asiya da Afrika.Najeriya da Nijar da Sudan Laberiya na cikin kasashen Afrika inda talauci da rashin kwanciyar hankali ke da nasaba da rashin zuwan makarantar tsakanin yaran da ake furgaban makomarsu. Akan wannan batu Umaymah Sani Abdulmumin ta zanta da Abdu Dan Naito, dan rajin kare hakkin bil’adama a Jamhuriyar Niger.