Isa ga babban shafi
China

China ta rattaba hannu kan yarjejeniyar Paris

China ce ta faarko wajen fitar da hayakin da ke gurbata muhalli a duniya
China ce ta faarko wajen fitar da hayakin da ke gurbata muhalli a duniya AFP/
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
1 min

Kasar China ta rattaba hannu kan yarjejeniyar dimamar yanayi da aka cimma a birnin Paris na Faransa, abinda ake ganin zai taka rawa wajen yaki da sauyin yanayin a duniya.

Talla

China ce ke kan gaba wajen fitar da hayaki mai gurbata muhalli a duniya, inda take fitar da kashi 25 cikin 100, yayin da Amurka ke bi mata da kashi 15 cikin 100.

A watan Disamban bara ne dai, Kasashen duniya 175 suka cimma yarjejeniyar a Paris, amma kawo yanzu, 24 ne daga cikinsu suka rattaba hannu don amincewa da ita a hukumance.

Ita ma Amurka ana saran za ta sanar da rattaba hannunta nan bada jimawa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.