Zika

Shawarar da MDD ta bayar game da cutar Zika

Masana kiwon lafiya na ci gaba da gudanar da bincike kan cutar Zika
Masana kiwon lafiya na ci gaba da gudanar da bincike kan cutar Zika Scott Olson/Getty Images/AFP

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci duk wani mutumin da ya ziyarci kasahsen da aka samu bullar cutar Zika da ya kauce wa jima’i na watanni 6 ko kuma ya yi amfani da kwaroron roba.

Talla

Hukumar ta ce matakin ya biyo bayan karin shaidun da aka samu ne, na cewar ana iya kamuwa da cutar cikin wannan lokaci sabanin binciken da aka yi a baya.

Hukumar ta kuma bukaci gwamnatocin kasashen da aka samu barkewar cutar da su baiwa al’ummarsu shawarar kauce wa yaduwar cutar ta hanyar jima’i.

A bangare guda, an samu mace ta farko mai juna biyu dauke da cutar ta Zika a Malaysia wadda rahotanni suka ce 'yar wata jiha ce mai makwabtaka da kasar Singapore, inda aka samu mutane 275 da suka kamu da cutar.

Mata masu juna biyu da ke dauke da cutar, na haihuwar jarirai da kananan kawuna tare da nakasa a halittarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI