UNICEF

Yara miliyan 50 sun kaurace wa gidajensu saboda yaki

Kananan yara miliyan 50 sun kaurace wa gidajensu saboda yaki da wasu matsalolin rayuwa
Kananan yara miliyan 50 sun kaurace wa gidajensu saboda yaki da wasu matsalolin rayuwa Unicef.fr

Hukumar Kula da ilimin kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF ta ce, akalla kananan yara miliyan 50 aka tilastawa kaurace wa gidajensu saboda yaki da tashe-tashen hankula da kuma azabtarwa.

Talla

Daraktan hukumar ta UNICEF Anthony Lake, ya bayyana halin da kananan yaran ke ciki a wata sanarwar da ya raba wa manema labarai inda yake cewa, hotunan Aylan Kurdi, dan kasar Syria da ya mutu a bakin teku da na Omran Dagneesh da aka jefa wa gidansu bam na daga cikin abubuwan da suka girgiza al'ummar duniya.

Jami’in ya ce, kowanne hotan yaro guda na nuna alamar miliyoyin yara ne da ke fuskantar hadari wanda ke bukatar daukar mataki dan kare lafiyarsu.

Hukumar ta ce, yara miliyan 28 tashin hankali ya raba da gidajensu, cikin su har da 'yan gudun hijira miliyan 10, yayin da ake da yara miliyan 17 da suka bar gidajensu a kasashen da suke saboda wasu dalilai.

Rahotan ya kuma ce, akwai yara miliyan 20 a duniya da rikicin kungiyoyi da kuma tsananin talauci suka raba da muhallansu, kuma yanzu haka ba su da matsuguni ko takardun shaida.

Hukumar ta ce a shekarar 2014 kawai, yara sama da  dubu 100 suka bar kasashensu ba tare da 'yan rakiya ba, inda suka bukaci mafaka a kasashe 78 na duniya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.