Brazil

'Yan Brazil sun yiwa sabon shugaban su Michel Temer ihu

Shugaban kasar Brazil Michel Temer
Shugaban kasar Brazil Michel Temer REUTERS/Ueslei Marcelino

'Yan Kasar Brazil sun yiwa sabon shugaban kasar su Michel Temer ihu lokacin da ake bikin ranar samun yancin kan kasar wanda ya kunshi faretin Soji.

Talla

Masu ihun sun yi ta shewar cewar ayi waje da Temer maci amana, yayin da magoyan bayan sa kuma ke jinjina masa.

Wannan dai shine aikin shugaban na farko a bainar jama’a tun bayan tsige shugabar kasar Dilma Rousseff.

Kazalika Shugaban ya sake fuskatar irin wannan ihun a yayin bude wasan Paralympic a Rio de Janeiro.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.