Amurka

MDD na gudanar da babban taronta a New York

Yau ake bude babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 71 a birnin New York, in da shugabannin kasahsen duniya za su mayar da hankali kan batun 'yan gudun hijira da kuma bakin da ke barin kasashensu dan samun rayuwa mai inganci.

Shugabannin kasashen duniya na gudanar fa taro a zauren Majalisar Dinkin Duniya, karo na 71 a birnin New York na Amurka
Shugabannin kasashen duniya na gudanar fa taro a zauren Majalisar Dinkin Duniya, karo na 71 a birnin New York na Amurka REUTERS/Mike Segar
Talla

Ana saran shugabanin kasahsen duniya su kwashe kwanaki masu zuwa wajen yin jawabi a taron.

A bangare guda, shugaban Amurka Barack Obama da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, za su yi jawabansu na karshe a matsayinsu na shugabanni a  taron na yau.

Jawabin Obama na zuwa ne a yayin da ya rage watanni biyu a gudanar da zaben Amurka, in da ake sa ran zai mayar da hankali kan yaki da kungiyar ISIS a Syria da Iraqi da kuma yaki da tsatsauran ra’ayi.

Ana kuma sa ran Obama zai jagoranci taron kaddamar da gidauniyar da za ta taimaka wa 'yan gudun hijira miliyan 21 da ke duniya.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon, shi ma zai kawo karshen aikinsa a ranar 31 ga watan Disamba, kuma wannan shi ne taro na karshe da zai jagoranta bayan kwashe shekaru 10 a kan karaga.

Sabbin shugabanin da za su halarci taron a karon farko, sun hada da Theresa May, sabuwar Firaministar Birtaniya tare da takwaranta na Canada, Justin Tradeau da shugaban Brazil Michell Temer.
 

Ana kuma sa ran jawabin shugabanin kasashen Turkiya da Iran, su dauke hankalin masu sa ido saboda matsayin kasashensu a siyasar duniya, sai kuma batun sasanta rikicin Gabas ta Tsakiya, in da ake ganin gazawar Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da shugaba Mahmud Abbas na Falasdinu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI