India-Faransa

India ta siyi jiragen yaki daga Faransa

Ministan tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian da takwaransa na India  Manohar Parrikar a birnin New Delhi
Ministan tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian da takwaransa na India Manohar Parrikar a birnin New Delhi REUTERS/Roberto Schmidt

Kasar India ta rattaba hannu kan yarjejeniyar siyan jiagen yakin Faransa samfurin Rafale guda 36 akan Dalar Amurka biliyan 8.8.

Talla

A yau ne ministan tsaron India, Manohar Parrikar da takwaransa na Faransa Jean Yvevs le Drian suka sanya kan yarjejeniar cinikikayyar a birnin New Delhi.

Wannan dai ita ce cinikayyar soji mafi grima da India ta yi a cikin shekaru da dama da suka wuce, yayin da masharta kan tsaro suka bayyana cewa, cinikayyar za ta inganta aikin sojin sama na India.

Tun a shekarar 2012 ne, kasashen biyu suka fara tattaunawa kan cinikayyar amma ta gamu da tangarda, in da a wancan lokacin India ta so siyan jiragen na yaki 126 daga Faransan.

Ana saran nan da shekarar 2019 ne, jiragen za su isa India don maye gurbin tsoffin jiragenta na yaki da ta siya daga Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.