Isa ga babban shafi
UNICEF

'Rayuwar yara na tsanani a kasashen masu tasowa'

Yara na rayuwa cikin matsanancin talauci
Yara na rayuwa cikin matsanancin talauci AFP/Albert Gonzalez Farran
Zubin rubutu: Umaymah Sani Abdulmumin
Minti 1

Bankin Duniya da Hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya sun ce akalla kashi daya bisa biyar na yaran da ke kasashe masu tasowa na rayuwa cikin matsanancin talauci.

Talla

Rahotan hukumomin biyu ya bayyana cewar kusan yara miliyan 385 ke rayuwa a kudin da ke kasa da Dala biyu kowacce rana, kuma akasarin su sun fito ne daga Afirka da Asia.

Jami’in UNICEF, Anthony Lake, ya bukaci gwamnatocin kasashen da abin ya shafa da su taimakawa iyayen yara dan inganta rayuwar su.

Majalisar Dinkin Duniya ta sanya shekarar 2030 a matsayin lokacin kauda tsananin talauci a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.