Amurka

Wikileaks zai fallasa sirrin siyasar Amurka

Hilary Clinton tare da Donald Trump da za su fafata a zaben Amurka mai zuwa
Hilary Clinton tare da Donald Trump da za su fafata a zaben Amurka mai zuwa REUTERS/Lucy Nicholson (L) and Jim Urquhart/File Photos

Shugaban shafin fallasa bayanan sirri na Wikileaks Julian Assange ya yi alkwarin fitar da sabbin bayanan sirri da suka shafi siyasar Amurka kafin gudanar da zaben shugabancin kasar.

Talla

Assange wanda ke magana a game da cikar kamfaninsa shekaru 10 da kafuwa, ya ce sabbin bayanan da yake shirin fitarwa za su shafi yadda ake zabe da kuma sauran batutuwa da ke da nasaba da haka a kasar ta Amurka.

A ranar 8 ga watan Nuwamba mai zuwa ne za a gudanar da zaben shuganbancin Amurka, in da ake saran Hilary Clinton ta jam’iyyar Democrat za ta fafata da abokin takararta Donald Trump na jam’iyyar Republican.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.