Isa ga babban shafi
Jamus-Nijar

Jamus za ta gina barikin soji a Nijar

Jamus za ta kafa sansanin soji a jamhuriyar Nijar don yaki da mayakan jihadi a Mali
Jamus za ta kafa sansanin soji a jamhuriyar Nijar don yaki da mayakan jihadi a Mali AFP PHOTO / DPA / PETER ENDIG
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
Minti 1

Kasar Jamus za ta gina wani barikin soji a cikin Jamhuriyar Nijar domin fada da ayyukan ta’addanci a makociyar kasar wato Mali.

Talla

Jakadan Jamus a birnin Yamai Bernd von Munchow-Pohl, wanda ke jawabi a game da zagayowar ranar da aka hade jamus ta gabas da kuma yamma, ya kuma ce, shugabar gwamnatin kasar Angela Merkel za ta ziyarci Nijar a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.
 

Kafin kasar ta Jamus, tuni kasashen Faransa da kuma Amurka suka gina nasu barikokin soji a kasar ta Nijar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.