Isa ga babban shafi
MDD

Canjin yanayi zai jefa mutane Miliyan 122 cikin Talauci

Kimanin mutane miliyan 14 ke fuskantar yunwa a kudancin Afrika saboda fari.
Kimanin mutane miliyan 14 ke fuskantar yunwa a kudancin Afrika saboda fari. WFP via twitter
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
Minti 2

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa matsalar sauyin yanayi na iya jefa mutane kusan miliyan 122 cikin matsanancin hali na talauci zuwa shekarar 2030. Kuma matsalar za ta fi shafar kananan manoma a kasashen Afrika da kudancin Asia.

Talla

A rahotan da ta ke fitarwa duk shekara hukumar FAO da ke kula da abinci da ayyukan noma ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa matsalar sauyin yanayi zai haifar da mummunar matsala da ba a taba gani ba ga al’umomin da ke dogaro da aikin noma domin samun abincinsu.

Hukumar FAO ta yi kira ga samar da wani tsarin noma da zai yi daidai da dumamar yanayi tare da lunka lunka tallafi ga kananan manoma kimanin miliyan 475.

Shugaban hukumar Jose Graziano ya ce babu shakka sauyin yanayi sai shafi abinci.

Sannan ya ce babban kalubale shi ne yadda a yanzu ba za su iya bayar da tabbacin ko za a iya girbe abin da aka shuka ba.

Hukumar FAO ta bukaci a rungumi sabbin dubarun da ta yi hasashe za su taimaka wajen kaucewa matsalar sauyin yanayi.

FAO ta bukaci kasashen da suka sanya hannu kan yarjejeniyar Paris su bullo da wasu sabbin dubaru tare tallafawa kananan kasashe wadanda masana’untun manyan kasashe ke gurbatawa muhalli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.