Isa ga babban shafi
DRC

Tarayyar Turai za ta sanya wa Congo takunkumi

Lokacin rikicin birnin Kinshasa  na Jamhuriyar Demokradiyar Congo da ya hallka mutane kimanin 50 a watan satumba
Lokacin rikicin birnin Kinshasa na Jamhuriyar Demokradiyar Congo da ya hallka mutane kimanin 50 a watan satumba AFP/EDUARDO SOTERAS
Minti 2

Kungiyar tarayyar Turai ta bukaci Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da ta gudanar da zabe nan da shekara mai zuwa ko kuma ta fuskanci sabbin takunkumai. 

Talla

A cikin watan Satumban da ya wuce ne, tarzoma ta barke a babban birnin Kishasa, in da kimanin mutane 50 suka rasa rayukansu bayan ‘yan adawa sun bukaci shugaba Joseph Kabila wanda ya dare kan karagar muki tun shekarar 2001 da ya sauka.

‘Yan adawar dai na fargaban yiwuwar Kabila ya zarce da mulki bayan karewar wa’adinsa a cikin watan Disamba mai zuwa.

Ministocin kasashen ketare na kungiyar, sun gana ne a wannan litinin  a Luxembourg, in da suka fara fitar da jerin sunayen ‘yan siyasan da ake ganin sun hana ruwa gudu wajen gudanar da zaben jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Majiyar tarayyar Turai ta ce, akwai bukatar tattara karin hujjoji don kakaba wa makusanta Kabila da ake zargi da kawo tarnaki a zaben takunkumai.

A bangare guda, ‘yan adawar kasar sun bukaci gudanar da yajin aikin game-gari nan da ranar laraba, a wani mataki na kara matsin lamba ga shugaba Kabila don ganin ya sauka daga karaga a cikin watan Disamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.