Spain

Kotun Spain ta goyi bayan hawan kaho

Wasan hawan kahon dai na haddasa asarar rayukam jama'a a Spain
Wasan hawan kahon dai na haddasa asarar rayukam jama'a a Spain AFP PHOTO/ ANDER GILLENEA

Kotun Kolin kasar Spain ta soke haramcin hana wasan hawan kahon da ya shahara a yankin Catalonia.

Talla

Kotun kolin ta ce, haramta hawan kahon wani yunkuri ne na kokarin dakushe al’adun mutanen yankin, wanda gwamnatin kasar ce ke da hurumi akai amma ba gwamnatin yanki ba.

Majalisar Catolonia ce ta kafa dokar haramta hawan kahon bayan wasu mutane dubu 180 sun gabatar da takardar korafi kan yadda ake cin zarafin dabbobi da kuma yadda shanu ke hallaka jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.