Isa ga babban shafi
UNICEF

Gurbataccen iska na kisan yara- UNICEF

Gurbataccen iska na cikin gida da waje da yara ke shaka na kisan kimanin 600,000 duk shekara
Gurbataccen iska na cikin gida da waje da yara ke shaka na kisan kimanin 600,000 duk shekara REUTERS/Edgard Garrido
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad | Awwal Ahmad Janyau
Minti 2

Hukumar kula da yara kanana ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta ce Yara kanana miliyan 300, daya daga cikin bakwai a duniya ke shakar gurbataccen iska, wanda ke haifar da yawan mace macen kananan yaran.

Talla

Rahoton na UNICEF da aka wallafa a yau litinin ya bayyana cewa yaran na rayuwa ne a inda gurbataccen iska ya zarce da kashi shida na mizanin da hukumar lafiya ta duniya WHO ta amince.

Binciken rahoton ya gano cewa kimanin yara biliyan 2 ke fama da matsalolin shakar iska da ke dauke da kura mai guba da ke fitowa daga ababen hawa.

Rahoton ya kuma bayyana cewa gurbataccen iskan na cikin gida da waje da yara ke shaka na kisan kimanin 600,000 duk shekara tare da haifar da cututtuka da suka shafi huhu.

Mafi yawanci matsalar ta fi shafar kasashen kudancin Asiya a cewar rahoton.

UNICEF ta yi kira ga gwamnatocin kasashe 200 da za su halarci taron tattauna canjyin yanayi a ranar 7 ga watan Nuwamba a Morocco da su dauki matakai domin inganta lafiya tare da rage dumamar yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.