Turai- Birtaniya

Birtaniya za ta daukaka kara kan ficewarta daga EU

Firaministar Birtaniya Theresa May
Firaministar Birtaniya Theresa May REUTERS/Kirsty Wigglesworth/pool

Gwamnatin Birtaniya za ta kalubalanci hukuncin da alkalan kasar suka yanke game da ficewar kasar daga kungiyar tarayyar Turai, in da suka bukaci majalisar dokoki ta kada kuri’a kafin fara shirin ficewa baki daya.

Talla

A makon jiya ne wata babbar kotun kasar ta yanke hukuncin cewa, dole sai majalisar dokokin kasar ta kada kuri’a don amincewa da shirye-shiryen ficewa daga kasashen Turai, abin da ake ganin zai kara haifar da jinkirin ficewar a kan lokaci.

Jaridar Daily Mail ta bayyana alkalan da suka yanke wanna hukunacin a matsayin makiyan al’umma, yayin da Nigel Farage na jam’iyyar UK independence ya gargadi gudanar da zanga-zanga akan tituna makatukar aka yi watsi da sakamakon kuri’ar jin ra’ayoyin jama’a da aka gudanar a can baya.

To sai dai gwamnatin firaminista Theraesa May ta ce, za ta daukaka kara a kotun Koli a cikin watan gobe bayan ta tanadi kwararan hujjoji don ganin an sauya hukuncin.
 

A cewar gwamnatin, ministocin kasar na da cikakken hurumin daukan mataki kan wannan batu ba tare da majalisar ta jefa wata kuri’a ba.

Hukuncin babbar kotun dai ya bukaci majalisar dokokin ta kada kuri’ar ne don sanin lokacin da Birtaniya za ta samu hurumin aiwatar da doka ta 50 da aka shata a karkashin yarjejeniyar Lisbon, wadda ta bai wa kasar damar zantawa da kasashen Turai don ficewa kai tsaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.