Amurka

Amurka ta yi watsi da yunkurin ICC kan sojinta

Ana zargin sojin Amurka da cin zarafin bil adama a Afghanistan
Ana zargin sojin Amurka da cin zarafin bil adama a Afghanistan AHMAD AL-RUBAYE / AFP

Kasar Amurka ta ce, ko kadan sojojinta da jami’an leken asirinta ba su aikata laifufukan yaki a kasar Afghanistan ba, saboda haka kotun hukunta manyan laifufuka ta duniya ba ta da hurumin gudanar da bincike a kansu.

Talla

Babbar mai gabatar da kara ta kotun Fatou Bensouda ta ce, tana nazari don gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa jami’an na Amurka na azabtar da mutane tsakanin shekarar 2003 zuwa 2004.

Amma mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka Elizabeth Trudeau ta ce, hawainiyar ICC ta kiyayi ramar Amurka, domin ita ba ta amince da halarcin kotun ba.

Wannan ya sa ake kallon Amurka a matsayin bakin-ganga, wadda ke bukatar ganin an hukunta 'yan wasu kasashe a kotun, amma kuma bata san a taba nata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.