Amurka

Trump ya yi barazanar rusa sulhun Cuba da Amurka

Zababben Shugaban Amurka Donald Trump
Zababben Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Jonathan Ernst

Shugaban mai jiran gado Donald Trump ya yi barazanar wargaza yarjejeniyar sulhun da Amurka ta kulla da Cuba idan har ba ta mutunta ‘yancin dan adam ba da bude kafar tattalin arzikinta.

Talla

Trump ya sanar da matakin ne a Twitter inda ya ce zai yi watsi da yarjejeniyar idan Cuba ba ta shirya amincewa da bukatun ci gaban mutanen Cuba da Amurkawa ba.

Trump ya yi barazanar rusa sulhun Cuba da Amurka

Sakon Trump bayan mutuwar tsohon shugaban Cuba Fidel Castro ya jefa shakku ga makomar dangantar Amurka da Cuba da Obama ya farfado da ita bayan shafe shekaru 50 suna gaba.

Trump ya soki marigayi Fidel Castro a matsayin shugaban kama-karya.

Trump dai na ganin gwamnatin Obama ta mika wuya sosai ga Cuba musamman kan dage takunkumin da Amurka ta kakabawa kasar tun a 1962.

Cuba bayan mutuwar Fidel Castro

Marigayi Fidel Castro dai shi ya jagoranci juyin juya halin da jam’iyyar kwaminasanci ta yi a shekarar 1959, wanda ya gina gwamnatin da ta taka gagarumar rawa wajen bunkasa Cuba da jama’ar ta.

Castro ya inganta samar da ilimi a Cuba da kula da lafiyar jama’ar kasar da kuma samar da rayuwa mai inganci abin da ya sa ya samu farin jini a tsakanin al’ummarsa.

Duk da cewa Castro ya mika mulkin kasar ga kaninsa Raul Castro a shekarar 2006 saboda dalili na rashin koshin lafiya ana dai ganin shi ke tafiyar da mulki ganin tsarin gwamnatin bai sha banban da na shi ba.

Sai dai manazarta na ganin yanzu akwai yiyuwar Raul Castro ya canja salon mulkin kasar sanadiyar mutuwar Fidel Castro a karshen makon da ya gabata

Raul Castro ya kafa tarihin ya dinke barakar da ke tsakanin Amurka da kasar a shekarar 2014, kasar da ta sanyawa Cuba takunkumin tattalin arziki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI