Faransa

"Faransa ta kashe Belmokhtar a harin sama"

Mokhtar Belmokhtar kwamandan Al qaeda reshen Afrika
Mokhtar Belmokhtar kwamandan Al qaeda reshen Afrika REUTERS

Wani rahotan asiri ya ce akwai alamun harin jiragen yakin Faransa ya hallaka shugaban kungiyar Al Qaeda reshen Afirka Mokhtar Belmokhtar wanda Amurka ke nema ruwa a jallo.

Talla

Wani jami’in Amurka ne da ba a bayyana sunan shi ba, ya tabbatar wa jaridar Wall Street Journal cewa bayanan sirrin Amurka sun taimakawa Faransa kashe Mokhtar Belmokhtar mai ido guda.

Labarin kisan Kwamandan na Al Qaeda a Afrika na zuwa a yayin da ministan tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian ke shirin tattaunawa da takwaransa na Amurka Ash Carter.

Labarin kashe Belmokhtar dai ya zama abin taka-tsantsan, ganin sau da yawa an sha ikirarin kashe shi amma daga baya sai ya sake bayyana da rai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.