Isa ga babban shafi
Cuba

Shugabanni masu ra’ayin Castro sun hadu a Cuba

Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe na cikin shugabannin kasashen duniya da suka halarci taron karrama Fidel Castro a Havana
Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe na cikin shugabannin kasashen duniya da suka halarci taron karrama Fidel Castro a Havana REUTERS
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau | Bashir Ibrahim Idris
Minti 2

Shugabannin kasashen kudancin Amurka da wasu takwarorinsu na Afirka ne suka halarci wani taron dubban mutane a Havana domin karrama tsohon shugaban kasar Cuba Fidel Castro da ya rasu yana da shekaru 90.

Talla

Shugabanin sun yi ta jawabi inda suke jaddada irin gudumawar da Castro ya bayar na tabbatar da juyin juya halin da ya zama fitila ga kasashen duniya da dama.

Cikin shugabanin da suka halarci taron sun hada da shugaba Rafael Correa na Ecuador da Evo Morales na Bolivia da Jacob Zuma na Afirka ta kudu da Nicolas Maduro na Venezuela da Daniel Ortega na Nicaragua da Robert Mugabe na Zimbabwe.

Gangamin shi ne na karshe a kwanaki biyu na karrama Fidel Castro kafin a fara yawo da tokar gawar tsohon shugaban na Cuba a sassan kasar na tsawon kwanaki hudu.

Firaministan Girka ne daga Turai ya halarci taron a Cuba, yayin da shugabannin manyan kasashen yammaci suka kauracewa taron.

Kasashen Rasha da China da Iran ma da ke amintaka da tsohon shugaban sun aika da wakilai ne.

Marigayi Castro dai ya shafe tsawon shekaru 50 yana adawa da Amurka wanda ya jefa duniya cikin barazanar yakin nukiliya a tsakanin 1962 zamanin yakin cacar baka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.