Amurka

China ta fusata game da tattaunawar Trump da shugabar yankin Taiwan

Zababben shugaban Amurka Donald Trump
Zababben shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Carlo Allegri/File Photo

China ta ce matakin da zababben shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na yin tattaunawa kai-tsaye ta wayar tarho da shugabar yankin Taiwan, abu ne da ba zai iya canza matsayin wannan yanki ba, wanda China ke kallo a matsayin wani bangare na kasarta.

Talla

Wannan dai ya kasance karo na farko a cikin shekaru 37 da wani shugaba na Amurka ya tattaunawa ta wayar tarho kai tsaye da shugaban yankin na Taiwan, bayan da aka yanke alakar diflomasiyya ta kai-tsaye tsakanin Amurka da Taiwan.

Trump dai ya bayyana a shafinsa na Tweeter cewa, shugabar yankin na Taiwan Tsai Ing-wen ta kira shi ta waya domin taya shi murnar nasara a zaben da ya lashe.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.