Isa ga babban shafi
Isra'ila-MDD

MDD ta haramta wa Isra'ila gine-gine a yankin Falasdinu

MDD ta bukaci Isra'ila ta dai na mamaye a yankin Falasdinu
MDD ta bukaci Isra'ila ta dai na mamaye a yankin Falasdinu
Zubin rubutu: Umaymah Sani Abdulmumin
1 min

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya haramta wa Isra'ila gine-gine a yankin Falasdinawa, bayan kada kuri'ar amincewa da kudirin da Amurka wadda babbar kawar Isra'ilar ce, ta zama 'yar babu ruwanmu kan al'amarin.

Talla

Da yammacin jiya ne dai Kwamitin ya amince da wani kudirin hukuncin da ya bayyana shirin gine-gine na Isra'ila da yi wa dokokin kasa da kasa karan tsaye.

Tuni dai Firaiministan Isra'ila, Benyamin Natenyahu, ya yi Alla-wadai da hukuncin kwamitin inda ya ce zai yi aike tare da shugaban Amurka mai jiran gado, Donald Trump domin warware wannan hukuncin na MDD.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.