Turkiya

Turkiya ta fara shari'a kan yunkurin juyin mulki

Jami'an 'Yan sanda 30 na fuskantar shari'a a kotun Santanbul na Turkiya saboda zargin su da hannu a yunkurin juyin mulki.
Jami'an 'Yan sanda 30 na fuskantar shari'a a kotun Santanbul na Turkiya saboda zargin su da hannu a yunkurin juyin mulki. REUTERS/Osman Orsal

Kimanin ‘Yan sanda 30 ne aka fara shari’arsu a kasar Turkiya a yau Talata da ake zargi da hannu a juyin mulkin da aka murkushe a ranar 15 ga watan Yuli, wanda shi ne karon farko da aka gurfanar daga cikin dubban mutanen da gwamnatin Recep Tayyip Erdogan ta kame. 

Talla

Ana sa ran kai wa zuwa ranar Juma’a ana muhawara a kotu, kuma yawancin ‘yan sandan na iya fuskantar hukuncin daurin rai da rai.

Kimanin mutane dubu 41 aka kame da ake zargi da hannu a yukurin juyin mulkin.

Ana zaman sauraren shari’ar ne a kotun Silivri da ke gidan yarin birnin Santanbul, yayin da ake ganin shari'ar a matsayin mai cike da sarkakiya.

Daga cikin wadanda aka kama kuma ake sa ran gurfanar da su nan gaba, sun hada da malaman makaranta da jami'an tsaro da wasu daga cikin ma'aikatan gwamnati, yayin da kuma ake zargin wani malamin addinin Islama Fethullah Gulen da kitsa juyin mulkin

Sai dai malamin wanda Amurka ta ki amincewa ta mika shi ga Turkiya ya musanta zargin da ake masa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.