Syria

Yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki a Syria

An shafe shekaru 5 ana yaki a Syria
An shafe shekaru 5 ana yaki a Syria REUTERS/Umit Bektas

Gwamnatin Syria da ‘yan tawayen kasar sun mutunta yarjejeniyar tsagaita buda wuta da da ta fara aiki a cikin daren Alhamis, matakin zai ba bangarorin biyu damar zama kan teburin sulhu da nufin magance rikicin kasar.

Talla

Shugaban Rasha Vladimir Putin ne ya fara sanar da yarjejeniyar kafin daga bisani kasar Turkiya ta tabbatar da ita.

Sai dai rahotanni sun ce, wannan yarjejeniyar tsagaita musayar wuta, ba ta shafi yankunan da mayakan IS ke tayar da kayar ba yaba.

Majalisar Dinkin Duniya ta yaba da yarjejeniyar tare da bayyana fatar ganin ta kasance matakin kawo karshen rikicin Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI