Amurka-Mexico

FBI na farautar wanda ya harbi jami'in jakadancin Amurka

Hukumar FBI za ta bada tukuicin dala dubu 20 ga duk wanda ya taimakata gano dan bindigan Mexico
Hukumar FBI za ta bada tukuicin dala dubu 20 ga duk wanda ya taimakata gano dan bindigan Mexico REUTERS/Shannon Stapleton

‘Yansanda a Mexico na farautar dan bindigan da ya harbi wani jami’in jakadanci Amurka a kasar a lokacin da ya ke kokarin tuki a yammacin kasar na Guadalajara.

Talla

Wani fai-fan bidiyo da aka wallafa a shafin facebook ya nuna yadda dan bindigar sanye da shudiyar riga, ya jikkata jami’in sakamakon budewa motarsa wuta kafin ya tsere.

Jama’in tsaron FBI da ke Amurka sun ware tukuicin dala dubu 20 ga duk wanda ya taimaka musu cafke dan bindigan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.