Isa ga babban shafi
Isra'ila

Mahari ya kashe sojojin Isra'ila 4 ta hanyar taka su da mota

Jami'an tsaron Isra'ila a birnin Quds
Jami'an tsaron Isra'ila a birnin Quds REUTERS/Ronen Zvulun
Zubin rubutu: Salissou Hamissou
1 min

Sojojin Isra'ila 4 ne suka cimma ajalinsu a wannan lahadi lokacin da wata babbar motar dakon kaya ta bi ta kan gungun sojojin a birnin Jérusalem, daya daga cikin hare haren karshe, da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tun farkon barkewar tashe-tashen hankullan a shekarar 2015.

Talla

Direban motar bafalesatine shi ma ya gamu da ajalinsa a yayin da wasu sojojin na Isra'Ila 15 suka jikkata daya daga cikinsu mummunan rauni.

Jami’an agaji sun bayyana cewa, sojojin da suka rasa rayukansu matasa ne 'yan mata hade da wani mai yawan shekaru 1

Tuni dai PM Isra'Ila Benjamin Natenyahu ya danganta harin da zama na ta’addanci, da wani dakaren kungiyar IS mai ikrarin jihadi ya kai.

 

Shi dai wannan hari ya wakkana ne a tsakkiyar ranar lahadi a kan wata doguwar hanya da jama a ke yawan kai kawo a kanta, da ke ba da damar hangen daukacin tsohon birnin na Jérusalem.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.