Amurka

Majalisar Amurka za ta tantance ministocin Trump

Donald Trump
Donald Trump REUTERS/Carlos Barria

Majalisar Dattawan Amurka za ta fara zaman tantance mutanen da shugaban kasar mai jiran gado Donald Trump ya gabatar don nada su a manyan mukaman gwamnatinsa.

Talla

Zaman tantance mutanen da za a fara a wannan Talatar, na a matsayin zakaran gwajin dafi da zai nuna kwarewar Trump wajen aiki tare da mambobin jam’iyyarsa ta Republican da ke majalisar.
 

Babban kalubalan da ke gaban Trump shi ne, tabbatar da cewa, mambobin majalisar 52 daga cikin 100 sun hada kawunansu don goyon bayan kafa majalisar ministocinsa, abin da zai saukake masa karbar mulki daga hannun shugaba Barack Obama na Democrat a ranar 20 ga wannan wata na Janairu.

Ana ganin cewa, zaman tantacewar zai bai wa ‘ya’yan jam’iyyar Democrat da ke majalisar damar cilla tambayoyi kan shirin Trump dangane da karbar baki da kuma gina katanga akan iyakar Amurka da Mexico.

Mutane bakwai ne dai ake sa ran tantance su a cikin wannan makon da suka hada da Sanata Jeff Sessions a matsayin Atoni Janar da kuma Janar John Kelly a matsayin ministan tsaron cikin gidan Amurka, sai kuma Rex Tillerson da za a tantance a matsayin sakataren harkokin wajen kasar.

Mai magana da yawun Donald Trump, Sean Spicer ya ce, ya yi amanna za a tabbatar da dukkanin mutanen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.