Iran-Nukiliya

Kasashen duniya sun gana da Iran kan Nukiliya

Zauren tattaunawa tsakanin manyan kasashen duniya da Iran kan batun nukiliya
Zauren tattaunawa tsakanin manyan kasashen duniya da Iran kan batun nukiliya REUTERS/Leonhard Foeger

Kasar Iran da manyan kasashen duniya sun gana a birnin Vienna don nazari kan yarjejeniyar makamashin Nukiliya da suka cimma a shekarar 2015. Sai dai batun rantsar da Donald Trump a matsayin sabon shugaban Amurka da kuma rasuwar tsohon shugaban Iran Akbar Rafsanjani za su iya shafar makomar wannan yarjejeniya. 

Talla

Donald Trump da zai sha rantsuwar kama aiki a ranar 20 ga wanna wata na Janairu, ya lashi takobin warware yarjejeniyar ta Nukiliya tsakanin Iran da manyan kasashen na duniya.

Rasuwar tsohon shugaban Iran Akbar Hashemi Rafsanjani da ya bar duniya yana da shekaru 82, ta sa an yi rashin bababn jigo mai matsakaicin ra’ayi da ke goyon bayan wannan yarjejeniya.

Ganawar da aka yi a birnin Vienna, in da aka cimma wannan yarjejeniya a cikin watan Julin 2015, ta samu halartar manyan jami’an doiflomasiyar Iran da Amurka da Rasha da China da Birtaniya da Faransa da kuma Jamus.

A karo na hudu kenan da kasashen suka gudanar da irin wannan zaman don nazari kan ci gaban da aka samu wajen aiwatar da yarjejeniyar wadda ta fara aiki gadan-gadan a cikin watan Janairun bara, kuma Iran ce ta buakci sake zaman bayan takunkumin da Amurka ta sabanta a kanta.

Duk da dai an dakatar da takunkumin na man fetir da kuma iskar gasa, amma dai kasar ta Iran na ci gaba da kallon matakin a matsayin warware yarjejeniyar ta Nukiliya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.