MDD

Guterres ya bukaci hadin kan kasashen duniya

Sabon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres
Sabon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres REUTERS/Stephanie Keith

Sabon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci hadin kan kasashen duniya don warware rikice-rikicen da ake fama da su a sassan duniya. Sakataren ya yi wannan kiran ne a ya yin jawabinsa na farko da ya gabatar a gaban kwamitin tsaro na majalisar bayan ya kama aiki. 

Talla

Mr. Guterres wanda ya fara aiki a ranar 1 ga watan Janairu, ya sha alwashin bai wa duniya mamaki wajen warware rikice-rikicen da ake fama da su da suka hada da rikicin Syria da kuma na Sudan ta Kudu.

Guterres ya ce lokaci ya yi da za a kawo karshen barnatar da tarin dukiya da kuma mayar da martani kan yake-yake.

Ana sa ran babban magatakardar ya fi maida hankali kan jagorancin shiga tsakani wajen warware rikice-rikicen da ke aukuwa a sassan duniya fiye da tsohon sakataren majalisar Ban Ki-oon da ya fi tura tawaga maimakon ya jogoranta da kansa.

A yanzu dai sabon sakataren zai fuskanci kalubalen hada kan kasashen da suka gina kwamitin tsaron majalisar, wadanda banbancin da ke tsakaninsu ya taimaka wajen tsaikon da aka samu na warware rikicin kasar Syria da ya shiga shekara ta shida ana fama da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.