Gabas ta tsakkiya

Kasashen duniya 75 na taron neman zaman lafiyar Isra'ila da Falsdinawa

Taron neman zaman lafiya a gabas ta tsakkiya na birnin  Paris, France. 15,01,2017.
Taron neman zaman lafiya a gabas ta tsakkiya na birnin Paris, France. 15,01,2017. Reuters/路透社

Kasashen duniya sama da 70 ne suka sake jaddada goyon bayansu ga Israela da Palestinawa, a lokacin wani taron da aka soma a yau lahadi a birnin paris na Fransa , taron ya kuma yi kashedi kan matakin da sabon shugaban kasar Amruka Donald Trump ke shirin dauka na amincewa da birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar Isra’ila.

Talla

Shawarar samar da kasashe biyu har yanzu ita ce manufar kasashen duniya, a cewar shugaban kasar Fransa Francois hollande a jawabin da ya gabatar wa wakilan kasashe 75 tare da na kungiyoyi masu zaman kansu, da suka halarci zaman taron da zummar samar da mafita ga rikicin Isra’ila da Falestinawa da bai samu halarta bangarorin da abin ya shafa ba.

Hollande ya ce, shiga tattaunawa kai tsakanin Isra’ila da palestinawa kawai ne zai bada damar cimma zaman lafiya a tsakaninsu, ba bu kuma wanda zai yi haka a madadinsu sai su da kansu. Hollande ya bayyana haka ne, a matsayin amsa ga kakkausar sukar da Isareala ta yi zaman taron na Paris.

Wannan dai ya biyo bayan kashedin da firayi ministan Fransa Jean-Marc Ayrault ya yi ne, kan abin da zai iya biwo bayan aiwatar da barazanar da shugaban kasar Amruka mai jiran gado, Donald Trump ya yi cewa, zai mayar da ofishin jakadancin Amruka dake birnin Tel Aviv zuwa na Jérusalem.Sai dai kuma kasar Britaniya ta ki saka hannu kan sanarwar bayan zaman wannan taro na birnin paris

a nata bangaren a cikin wata sanarwa ma’aikatar harakokin wajen kasar  Birtaniya ta ce kasar na da shakku a kan  taron, lura da yadda wadanda ake yi dominsu ba su halarce shi ba, haka kuma taro ne da ake gudana  ba tare da son ran  Israela ba, don haka Birtaniya ta halarci taron ne a matsayin yar kallo.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.