Amurka

Democrats za ta kauracewa bikin rantsar da Trump

Shugaban kasar Amurka mai jiran gado Donald Trump
Shugaban kasar Amurka mai jiran gado Donald Trump REUTERS/Mike Segar

Akalla 'yan jam’iyyar Democrats 26 ne suka ce zasu kauracewa bikin rantsar da zababben shugaban Amurka Donald Trump. Da dama sun ce sukar da Trump ya yi wa mai rajin kare hakkin dan adam John Lewis na daga cikin dalilan da zai hanasu halartar bikin da za a gudanar wannan juma'ar.

Talla

Shugaba mai jiran gado Donald Trump dai ya soki Mista John Lewis, inda ya ce babu abinda dan rajin kare hakkin dan adam din ya sani face surutu.

Kalaman na Trump sun matukar bakantawa al’ummar kasar da dama rai ganin yadda ake mutunta Mista Lewis bisa gwagwarmayasa ta samar da daidaito tsakanin Amurkawa musanman damar bai wa bakakken fata 'yan-ci da sauran al’ummar kasar.

Mista Trump ya soki Lewis ne a daidai lokacin da al’ummar kasar ke shirin bikin ranar shaharraren bakar fatar Amurka Martin Luther King.

Wannan dai shine karon farko a tsawon shekaru talatin da Lewis ya kasance dan Majalisa da ba zai halarci bikin rantsar da shugaban kasar Amurka ba.

Batun kutsen Rasha a zaben Amurka na daga cikin dalilan da Mista Lewis ya bayar na kin halartar bikin abinda ya fusata Trump har ya ci zarafinsa a shafinsa na twitter.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.