Turai

Amnesty ta koka kan yanayin yaki da ta'addanci

Amnesty International ta nuna damuwa kan yadda ake cin zarafin bil'adama da sunan yaki da ta'addanci a kasashen Turai
Amnesty International ta nuna damuwa kan yadda ake cin zarafin bil'adama da sunan yaki da ta'addanci a kasashen Turai Logo AI

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta nuna damuwa kan yadda ake cin zarafin mutane da sunan yaki da ta’addanci a kasashen Turai.

Talla

A cikin wani rahoto da ta fitar a jiya Talata, Amnesty International ta bada misali da wani dan asalin kasar Syria mai suna Ahmed, da aka yanke wa hukuncin daurisn shekaru 10 a karshen watan Nuwamban da ya gabata saboda zargin sa da aikin ta’addanci.

Amnesty ta bayyana shari’ar Ahmed a matsayin abin kunya da ke nuna yadda ake tauye hakkokkin jama’a.

Kungiyar ta ce an daure Ahmed ne mazaunin Cyprus da ya taimaka wa iyayensa ficewa daga Syria mai fama da rikici, bayan an zarge shi da jifan ‘yan sanda da duwatsu a yayin wata tarzoma da ta barke a shekarar 2015, lokacin da wasu ‘yan gudun hijira suka yi kokarin tsallaka katangar iyakar Hungary da Serbia.

Kazalika an zargi Ahmed da yin amfani da amsa-kuwa a yayin tarzomar, zargin da hukumomi suka gaza tantance gaskiyarsa, in ji Amnesty.

Amma duk da haka kotu ta yanke masa hukunci ba tare da la’akari da hujjojin da ka iya wanke shi ba kamar yadda Amnesty ta ce.

Amnesty ta ce, wannan lamari ya nuna girmar matsalar keta hakkin dan Adam a Turai da sunan yaki da ta’addanci.

Amnesty ta ce, dokokin na yaki da ta’addancin a kasashen na Turai sun yi wa dokokin kare hakkin bil’adama hawan kawara.

Direktan Amnesty a nahiyar Turai John Dalhuisen ya ce, Faransa da ta rasa mutane 238 a hare-haren ta’addanci tun daga shekarar 2015, ta taka rawa wajen tsaurara wannan doka , yayin da Hungary da Bulgaria da Poland da Luxembourg suka yi koyi da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.