Amurka

Obama ya yi wa Chelsea Manning sassauci

Chelsea Manning da ta fallasa sirrin Amurka ga Wikileaks
Chelsea Manning da ta fallasa sirrin Amurka ga Wikileaks REUTERS

Shugaban Amurka mai barin gado Barack Obama ya rage wa’adin zaman gidan kaso da aka yanke wa Chelsea Manning da aka samu da laifin fallasa bayanan sirrin kasar ga shafin Wikileaks a shekarar 2010.

Talla

Yanzu haka Manning da aka yanke wa hukuncin daurin shekaru 35 a shekarar 2013, za a sake ta a ranar 17 ga watan Mayu mai zuwa.

Shugaba Obama ya yi wa Chelsea Manning rangwamen zama gidan kason ne a dai dai lokacin da ya rage ‘yan sa’oi wa’adinsa ya kare.

An dai yanke wa Manning hukuncin zama gidan kason ne har zuwa shekarar 2045 saboda rawar da ta taka wajen fallasa bayanan sirrin diflomasiya ga shafin na Wikileaks.

Fallasa bayanan da Manning ta yi na daya daga cikin manyan cin amana da aka taba yi wa Amurka a tarihinta kuma an yi mata sassaucin ne bayan jama’a sun bukaci haka, abin da kuma ya faranta wa danginta rai.

Chelsea Manning dai ta kasance na miji tun daga farkon rayuwarta amma daga bisani ta sauya kanta zuwa Mace, Kuma ana kiranta Bradley Manning a lokacin da ta ke amsa sunan na miji.

A can baya, shafin Wikileaks ya ce, shugabansa Julian Assange zai amince a tasa keyarsa zuwa Amurka matukar Obama ya yi wa Manning afuwa.

Jimillar mutane 209 ne shugaba Obama ya yi wa rangwamen zama gidan kaso, sannan kuma ya yi wa mutane 64 afuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.