Mexico-Amurka

Shugaban Mexico ya soke ganawa da Trump

Shugaban mexico ya soke ganawa da Donald Trump
Shugaban mexico ya soke ganawa da Donald Trump REUTERS/Carlos Jasso

Shugaban Mexico Enrique Pena Nieto, ya soke kai ziyarar aiki a Amurka domin ganawa da shugaba Donald Trump.

Talla

Soke ziyarar dai na kara fito da sabanin da ke tsakanin shugabannin biyu dangane da yunkurin gina katangar da za ta raba Amurka da Mexico.

Shugaban kasar ta Mexico Enrique Nieto da kansa ne ya sanar da soke kai ziyarar a shafinsa na Twitter, inda ya ce tuni ya sanar da takwaransa na Amurka Donald Trump hakan a hukumance.

Shugaban na Mexico ya ce bai kintsa wa ganawa da shugaban na Amurka domin tattauna batun gina katangar da za ta raba kasashen biyu ba, ganawar da ya kamata a yi a ranar talata.

Tun lokacin yakin neman zabensa, Trump ya sanar da cewa matukar ya yi nasara to daya daga cikin matakan da zai dauka sun hada da gaggauta gina katangar da za ta raba kasashen biyu, kuma zai yi haka ne domin hana kwarara baki zuwa cikin Amurka.

Bayan rantsar da shi kuwa, shugaban na Amurka ya jaddada wannan matsayi nasa, inda ya ce dole ne shugaban Mexico ya zo da shirin amincewa kasar shi ce za ta biya Amurka kudaden da za a kashe domin gina wannan katanga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.