Amurka

Trump ya kori babbar lauyar Amurka saboda baki

Sally Yates da shugaban Amurka, Donald Trump ya kora daga mukamin babbar lauyar kasar
Sally Yates da shugaban Amurka, Donald Trump ya kora daga mukamin babbar lauyar kasar alchetron.com

Shugaban Amurka Donald Trump ya kori babbar lauyar gwamnatin kasar Sally Yates saboda kin goyan bayan shirinsa na hana baki Musulmi shiga kasar.

Talla

Yates ta bayyana dokar a matsayin wadda ta ci karo da matsayinta na kare dokokin Amurka da kuma tabbatar da yi wa mutane adalci.

Jami’ar ta ce, a matsayin ta na babbar lauyar gwamnati, ba za ta iya kare dokar a kotu ba saboda ta saba ka’ida, kuma wannan ya sa Trump ya sanar da tube ta daga mukamin.

Yanzu haka dai, an nada Dana Boente a matsayin mukaddashin babban lauyan Amurka kafin majalisar dattawar kasar tabbatar da Sanata Jeff Sessions da Trump ya gabatar da sunansa don amincewa da shi a matsayin Atoni Janar.

Kasashen duniya na ci gaba da mayar da martani kan wannan mataki da Trump ya dauka na hana kasashen musulmi bakwai shiga cikin Amurka, abin da Majalisar Dinkin Duniya ta ce, ya saba ka'ida, kuma hakan zai haifar da cikas a yaki da ta'addanci a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.