EU- US

Hollande ya caccaki matsin lambar Trump kan EU

Shugaban Faransa Francois Hollande da ke halartar taron EU a Malta
Shugaban Faransa Francois Hollande da ke halartar taron EU a Malta AFP 法新社

Shugaban Faransa Francois Hollande ya caccaki abin da ya kira matsin lambar da takwaransa na Amurka Donald Trump ke yi wa kungiyar kasashen Turai.

Talla

Shugaba Hollande da ke magana a taron kungiyar kasashen Turai da ake gudanarwa a Malta, ya bayyana cewa, ba za su amince da matsin lambar daga Trump ba, wanda ya yi fatan rugujewar kungiyar tarayyar Turai.

Shugabannin na Turai 28 dai za su yi kokarin hada kawunansu don farfado da martabar nahiyar wadda ke fuskantar barazana daga ficewar Birtnaiya da kuma Donald Trump.

Taron na yau jumma’a shi ne irinsa na baya-bayan da Kungiyar Tarrayyar Turai ke gudanarwar tun bayan kuri’ar ficewar Birtaniya da al'ummar kasar ta kada a cikin watan Yunin bara.

Kazalika taron zai mayar da hankali kan matsalar bakin haure a dai dai lokacin da ake fargabar kwararowar dinbim jama’a da ke kasadar tsallaka teku daga Libya.

Shugaban Tarayyar Turai Donald Tusk ya ce, babban makasudin taron shi ne rage kwararar baki da ke ratsowa ta Libya zuwa Turai.

Tusk ya kara da cewa, dakile kwararar bakin, zai magance mutuwar mutanen da ke gamuwa da ajalinsu a sahara ko kuma teku bayan sun yi yunkurin shiga Turai don samun ingantacciyar rayuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI