Syria

Gwamnatin Syria da 'yan tawaye sun aikata laifukan yaki

Wani rahoton bincike na Majalisar Dinkin Duniya ya zargi gwamnati da kuma ‘yan tawayen Syria da aikata laifufukan yaki a lokacin da suke fafatawa da juna domin kama ikon birnin Aleppo.

Birnin  Aleppo na Syria
Birnin Aleppo na Syria Reuters/Khalil Ashawi
Talla

Rahoton ya kuma zargi bangarorin biyu da amfani da makami mai guba wajen kaddamar da farmaki da kashe fararen hula da kuma tirsasa wa jama’a kaurace wa muhallansu.
 

Kwamitin binciken dai ya mayar da hankali kan kawanyar da dakarun gwamnati suka yi wa birnin har tsawon watanni biyar tsakanin watan Yuli zuwa Disambar 2016, lokacin da dakarun suka karbe birnin daga hannun ‘yan tawayen.
 

Kwamitin ya ce, rundunar saman Syria da aminiyarta ta Rasha sun kaddamar da farmaki akai -akai a birnin na Aleppo.
 

Rahoton ya ce, akwai kwararan shedu da ke nuna yadda rundunar sojin saman Syria ta cilla makamai masu guba da suka hada da sinadarin Chlorine. Sai dai babu wani bayani da ke nuna cewa rundunar sojin Rasha ta yi amfani da makami mai guba.

Har ila yau binciken ya kuma gano cewa, gwamnatin Damascus ce ta kai hari kan ayarin motocin agaji a ranar 19 ga watan Satumba, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar ma’aikatan agaji 10.

A bangare guda, kwamitin ya ce, kungiyoyin ‘yan tawayen da suka hada da mayakan Fatal al Sham, sun yi lugudan wuta kan fararen hula a yankin yammacin Aleppo, in da kuma suka yi ta bude wuta babu kakkautawa kan mai uwa da wabi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI