Syria

Dakarun Syria sun karbe Palmyra daga hannun ISIS

Sojojin Syria a garin Palmyra mai dimbin tarihi
Sojojin Syria a garin Palmyra mai dimbin tarihi REUTERS/Omar Sanadiki

Dakarun Syria sun sake samun nasarar kwato tsohon birnin Palmyra daga hannun mayakan ISIS, tare da taimakon dakarun kawance da kuma jiragen yakin Rasha. 

Talla

A cikin watan Disamban bara ne kungiyar ISIS ta sake kwace birnin bayan watanni takwas da fatattakar ta daga cikinsa.

Kungiyar da ke sa ido kan hakkin dan Adamn a Syria ta ce, sojoji da kuma mayakan da ke samun goyon bayan Iran sun kutsa cikin Palmyra a ranar Alhamis bayan mayakan ISIS sun fice baki daya.

Kungiyar ta ce, mayakan na ISIS sun koma wasu yankuna da ke gabashin kasar, yayin da sojojin ke aikin tono nakiyoyin da aka binne a karkashin kasa a birnin na Palmyra mai cike da tarihi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.