Koriya ta Arewa-Amurka

Koriya ta Arewa ta gargadi Amurka da kada ta sake sanya ta cikin kasashen ta'addanci

Shugaban Koriya ta Arewa  Kim Jong Un
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un Reuters/路透社

Kasar Koriya ta Arewa ta gargadi Amurka da cewa zata yi da na sani muddin ta sake zana sunan kasar cikin jerin sunayen kasashen masu aikata ta'addanci, bayan kisan da aka yiwa wani dan uwan shugaban Koriya ta Arewa a kasar Malaysia.

Talla

Ranar 13 ga watan jiya aka kasha Kim Jong-Nam mai shekaru 45 a filin jiragen sama na Kuala Lumpur na kasar Malaysia.

Koriya ta kudu tuni ta ce jami'an Koriya ta Arewa na da hannu wajen wannan kisa.

Wasu kafofin labarai na Koriya ta Kudu da kasar Japan sun bayyana cewa mai yiwuwa ne Amurka ta cusa sunan Koriya ta Arewa cikin jerin sunayen kasashen dake da hatsari saboda ta'addanci.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI