Amurka

Trump ya zargi Obama da nadar zantukansa

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Jim Lo Scalzo/Pool

Shugaban Amurka Donald Trump ya zargi tsohon shugaban kasar wanda ya gada Barack Obama da nadar bayanan wayarsa a lokacin da ya ke yakin neman zabe.

Talla

Trump ya yi zargin ne a shafin shin a Twitter inda ya ce kwararren lauya zai ci kasuwa akan zahirin nadar bayanansa ta waya da Obama ya yi a watan Oktoba.

Sai dai kuma Trump ya yi zargin ne ba tare da gabatar da kwararan hujjoji.

Wannan dai na zuwa a yayin da Trump ke ci gaba da fuskantar baraka a gwamnatin shi bayan bankado ganawar da wasu manyan jami’ansa suka yi da jami’an diflomasiyar Rasha a lokacin yakin neman zabensa.

Gwamnatin Obama ta zargi Rasha da taimakawa Trump ta hanyar yin kutse a shafin jam’iyyar Democrat wanda ya dagula yakin neman zaben Hillary Clinton.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.