Amurka

Ana sa ran Trump ya gabatar da sabuwar dokar hana shiga Amurka a Litinin

Shugaban Amurka  Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Jim Lo Scalzo/Pool

A gobe littini ne ake saran Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu cikin doka na tsarin  hana shiga Amurkan, wata daya bayan kafa dokar da ta janyo suka daga ciki da wajen kasar wadda ta haifar da cunkoso a filayen jiragen saman kasar.

Talla

Babu Karin haske gameda irin sauye-sauyen da Shugaba Trump zai shigar cikin sabon matakin gameda shiga Amurka.

An zargi dokar da ya kafa ranar 27 ga watan Janairu na hana wasu ‘yan kasashen musulmi shiga Amurka cewa mataki ne kawai don nunawa musulmi kyama.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.