Firaministan Japan Shinzo Abe zai zarce da iko har shekara ta 2021.
Wallafawa ranar:
Wata sabuwar dokar da jam'iyar dake mulki a kasar Japan ta fito da shi ya baiwa Firaministan kasar Shinzo Abe ikon zarcewa da mulki har shekara ta 2021.
A yau lahadi jam'iyar ta LDP ta amince da sabon dokan a babban taron jiga-jigan Jamiyar da aka yi.
Karkashin tsohon tsarin Firaministan zai sauka a watan Satumba na badi koda jam'iyar ke mulki.
Karkashin sabon tsarin Firaministan na iya sake tsayawa takara a zaben badi da za'ayi.
Shinzo Abe mai shekaru 62 ya dana kujeran Firaminstan na kusan shekara daya amma ya sauka a shekara ta 2007 saboda rashin nasarar zabe a Babbar majalisar kasar.
A shekara ta 2012 ne kuma ya sake samun nasarar hawa kujeran Firaminista, bayan zama a bangaren adawa na shekaru uku.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu