Amurka

FBI ta yi watsi da zargin Trump akan Obama

Tsohon shugaban Amurka Barack Obama tare Donald Trump a ranar 20 ga Janairu da aka rantsar da shi a matsayin sabon shugaban Amurka
Tsohon shugaban Amurka Barack Obama tare Donald Trump a ranar 20 ga Janairu da aka rantsar da shi a matsayin sabon shugaban Amurka REUTERS/Carlos Barria/File Photo

Babban Daraktan hukumar bincike ta FBI a Amurka James Comey ya bukaci bangaren shari’ar kasar ya yi watsi da zargin da shugaba Donald Trump ya ke yi wa Barack Obama na nadarar zantukansa ta tarho kafin zabensa shugaban kasa.

Talla

Mista Comey ya yi watsi da zargin inda ya ce babu kamshin gaskiya ga zargin da Trump ke yi wa Obama kamar yadda kafofin yada labaran Amurka suka ruwaito.

Turmp da kansa ne ya zargi Barack Obama a shafin shi na Twitter da bayar da umurnin nadar hirarrakin da ya ke a wayarsa kafin zaben da aka yi cikin watan Nuwamban bara.

Tuni dai wani mai magana da yawun Obama ya musanta zargin.

Amma Trump ya bukaci majalisar dokokin kasar ta binciki zargin na saurare tare da nadar illahirin hirarrakin wayarsa a lokacin yakin neman zabensa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI