Amurka- Najeriya

Ba mu hana 'yan Najeriya zuwa kasarmu ba- Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump ya samar da dokar haramta wa wasu kasashe shiga cikin kasarsa
Shugaban Amurka Donald Trump ya samar da dokar haramta wa wasu kasashe shiga cikin kasarsa © REUTERS/Kevin Lamarque

Ofishin Jakadancin Amurka da ke Najeriya ya ce, bai hana 'yan Najeriya zuwa kasar ba, kuma duk wani mai dauke da bizar zuwa Amurka na iya zuwa ba tare da wata fargaba ba.

Talla

Wata sanarwar da Ofishin Jakadancin na Amurka da ke Abuja ya fitar, ta ce babu dalilin da zai sanya 'yan Najeriya da ke dauke da bizarsu fasa zuwa Amurka ko soke tafiyarsu saboda Najeriya ba ta cikin kasashen da sabuwar dokar hana shigar baki ta shafa.

Shi ma ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyema ya ce, babu wani sauyi da aka samu dangane da dangantakar da ta ke tsakanin kasashen biyu.

Daga cikin baki miliyan 2 da dubu 100 'yan Afrika da ke zama a Amurka a shekarar 2015, kididiga ta nuna cewar  dubu 327 'yan Najeriya ne.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.