Birtaniya

Auren dole ya karu a Birtaniya

An samu karuwar auren dole a Birtanida duk da dokar da ta haramta hakan a kasar
An samu karuwar auren dole a Birtanida duk da dokar da ta haramta hakan a kasar Getty Images

Wani rahoto da aka wallafa ya ce, an samu karuwar yawan adadin auren dole a Birtaniya a shekarar da ta gabata fiye da shekarun baya, yayin da kungiyoyin kare hakkin bil’adama suka ce adadin ya zarce 1,400 da aka ruwaito saboda yadda ake boye matsalar. 

Talla

Bangaren kula da auren dole a Birtaniya ya ce, ya samu bayanai kimanin 1,428 na auren dole a 2016 a ta hanyar sakon email da kuma kiran mutane a wayoyin salula.

Adadin dai ya zarce na 2015, in da aka samu yawan adadin auren dole kimanin 1220.

Rahoton ya ce, yawancin wadanda auren dolen ya shafa ‘yan kasa da shekaru 18 zuwa 24 ne.

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama da ke tattara bayanan auren dolen sun kara smaun kwarin guiwa ne saboda yawaitar mutanen da ke kawo rahoton auren dolen.

Dokar Birtaniya dai ta haramta auren dole ko da kuwa a kasashen waje aka daura auren, amma rahton ya ce, matsalar ta fi shafar mata ‘yan asalin kasashen kudancin Asia da suka kunshi Pakistan da Bangladesh da India da Afghanistan da Saudi Arabia sai kuma Somalia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI