Amurka

Jihohin Amurka za su kalubalanci dokar Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu kan dokar takaita shigar baki Amurka
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu kan dokar takaita shigar baki Amurka REUTERS/Jim Lo Scalzo/Pool

Jihohin Amurka da dama sun bayyana shirinsu na kalubalantar sabuwar dokar hana shigar baki daga kasashen Musulmi 6 da shugaba Donald Trump ya sanya wa hannu a wannan makon.

Talla

Jihohin New York da Washington da Oregon duk sun bayyana shirinsu na rugawa kotu don ganinsun hana dokar aiki kamar yadda aka hana irinta a farko.

Tuni Jihar Hawaii ta gabatar kararta don kalubalabtar dokar wadda ta bukaci dakatar da bada Bisa ga 'yan asalin kasashen Somalia da Syria da iran da Libya da Yemen da Sudan.

Jihohin tare da masu rajin kare hakkokin baki sun bayyana dokar a matsayin wadda ke nuna wariya ga al’ummar Musulmi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI